Kotu a jihar Kogi ta yanke ma wani gagararren dan sara suka hukuncin kisa ta wata hanya mai tsananin wahala

Kotu a jihar Kogi ta yanke ma wani gagararren dan sara suka hukuncin kisa ta wata hanya mai tsananin wahala

Wani fitinannen dan sara suka dake jagorantar wata gungun yan daba, Mohammed Audu ya gamu da hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan da Kotu ta kama shi da laifin kisan kai shi ma.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Kotun ta kama Audu ne da laifin kisan wani mutumi mai suna Husseini Isah a sakamakon wata rikici akan fili da ta taso, inda ya luma masa wuka a ciki.

KU KARANTA: Bincike: Gwamna Ganduje ya amince da ajiye aiki da babban akantan jihar Kano ta yi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin Kotun, kuma alkalin alkalai a jihar Kogi, Mai sharia Nasir Ajanah ne ya yanke hukuncin a ranar juma’a 23 ga watan Feburairu, inda yace: “Hukuncin ka shi ne za’a rataye ka har sai ka mutu, ko kuma a tsira maka allurar guba.”

Lauya mai kara ya shaida ma Kotu cewar Audu tare da wasu gungun yan daba su shida sun nufi zuwa wani fili da ake ta faman rigima akansa tsakanin daya daga cikin yan gugun nasa, Momoh Abaniki, da iyalan Husseini Isah, inda cacar baki ta kaure tsakaninsu da mamacin.

Bayan haka ne sai mamacin ya wuce gida, inda ya shaida ma yayansa, Ozovehe Isa lamarin, tare da sauran danginsa, amma sai Audu ya biyo shi gida, kuma yace masa shege ka fasa, kafin a Ankara ya sassara masa kai, inda sauran gungun suka diran masa da duka har sai da ya mutu.

Ganin hukuncin da yake fuskanta, sai Audu ya amsa laifinsa, inda ya bukaci a mai sassauci, cewar ba zai kara shiga miyagun harka ba, amma ina, bakin alkalami ya bushe, Alkali ya yanke hukunci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng