Kisan yaran Buni Yadi: Da kaina na kwashe zakulo gawan yarana biyu - Mahaifin ya yi tsokaci kan kisa daliban makarantan Buni Yadi 58

Kisan yaran Buni Yadi: Da kaina na kwashe zakulo gawan yarana biyu - Mahaifin ya yi tsokaci kan kisa daliban makarantan Buni Yadi 58

A ranan 24 ga watan Fabrairu, 2014, yan Boko Haram sun kai mumunan hari makarantan kwana a garin Buni Yadi inda suka hallaka dalibai 58.

Duk da cewa jama’an sun yi saurin mantawa da wannan mumunan hari, bayan watanni 2 aka kai sabon hari makarantan Chibok inda aka sace yan mata akalla 200 wadanda akafi sani da yan matan Chibok.

Goni Ali, mahaifin yara hudu ne a makaranta. An kashe masa yara biyu, ya bayyana yadda wannan abu yayi mayukar shafar rayuwansa.

“Da kanmu muka kwashe gawawwakin yaranmu kuma babu wanda ya taimaka mana. Ko jaje babu wanda yayiwa iyaye.

“Ma’aikatar ilimin jihar basu tuntubemu ba har sai bayan shekara daya. Na bayyana musu bacin ranmu akan abinda gwamnati tayi mana.”

Kisan yaran Buni Yadi: Da kaina na kwashe zakulo gawan yarana biyu - Mahaifin ya yi tsokaci kan kisa daliban makarantan Buni Yadi 58
Kisan yaran Buni Yadi: Da kaina na kwashe zakulo gawan yarana biyu - Mahaifin ya yi tsokaci kan kisa daliban makarantan Buni Yadi 58

Amma rahoto ya bayyana cewa gwamnan Ibrahim Geidam ya kai ziyara makarantan kuma ya baiwa iyayen yaran N100 million. Amma bisa ga abinda mahaifin ya fada, da alamun wannan kudin bai kai garesu ba.

KU KARANTA: An gurfanar da Al-Barnawi, shugaban 'Yan Ansaru, a gaban kotu a Abuja

Har ila yau, yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram na cigaba da addaban al’ummar yankin Arewa maso gabashin Najeriya. A makon nan sun kai sabon hari makarantan mata a garin Dapchi inda suka sace yan matan da har yanzu ba’a san adadinsu ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng