Cikin Hotuna: Olu na Warri ya ziyarci shugaba Buhari a fadar Villa
Sarki Olu na masarautar Warri ta jihar Delta, mai martaba Ogiame Ikenwole, ya jagoranci fadawan sa har zuwa fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya domin ganawa da shugaba kasa Muhammadu Buhari a yau Juma'a.
Rahotanni sun bayyana cewa, Olu ya sauka a fadar ne da misalin karfe 10.55 na safiyar yau Juma'a, inda aka tarairaye shi har zuwa babban ofishi na shugaba Buhari.
KARANTA KUMA: Sayayya 2 dana taba yi a rayuwata da ta wuce hankali - Bill Gates
Rahotanni da sanadin fadar shugaban kasa sun bayyana cewa, musabbabin wannan ziyara bai wuci batutuwan harkallar dake tsakanin kabilar Itsekiri da Ijaw dangane da sabuwar jami'ar Maritime da gwamnatin tarayya ta assasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng