Gwamnatin Jihar Yobe ta nemi afuwa akan 'yan matan Dapchi

Gwamnatin Jihar Yobe ta nemi afuwa akan 'yan matan Dapchi

- Gwamnatin Jihar Yobe ta nemi afuwan akan labarin ceto 'yan matan Dapchi

- Gwamnan jihar ya kai ziyara garin na Dapchi a jiya Alhamis

- Ya bukaci iyalan yaran da su cigaba da addu'a da kuma bawa gwamnati goyon baya domin samun mafita

Gwamnatin Jihar Yobe ta nemi afuwa akan 'yan matan Dapchi
Gwamnatin Jihar Yobe ta nemi afuwa akan 'yan matan Dapchi

Gwamnatin Jihar Yobe ta nemi afuwa ga ga rahoton da gwamnatin jihar ta fitar wanda babu gaskiya a cikin shi, da yake nuna cewa an ceto wasu daga cikin 'yan matan da aka sace a jihar. A kalla 'yan mata 30 ne aka sace, a wata Kwalejin Kimiyya ta mata dake Dapchi, a jihar ta Yobe, hakan ya biyo bayan wani hari da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram sun kai makarantar.

DUBA WANNAN: Babbar akawun jihar Kano ta ajiye aikinta

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Laraban nan ta bayyana cewa an ceto da yawa daga cikin 'yan matan da aka sace din, wanda daga baya aka gano cewar labarin karya ne.

Gwamnatin jihar ta nemi gafarar mutane akan labarin na nuna cewa labarin ba gaskiya bane a ranar Alhamis dinnan data gabata. Jama'a na iya tunawa da cewa mun bayar da sanarwa a daren jiya na cewa an samu damar ceto wasu daga cikin 'yan matan da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace a makarantar sakandare dake Dapchi.

Gwamnan jihar Ibrahim Gaidam yaje garin Dapchi a jiya, inda ya zauna tare da manyan garin da kuma shugabannin makarantar. Gwamnan kuma ya roki iyayen yaran da ba a gansu ba da su yi hakuri kuma su cigaba da addu'a, yayin da gwamnati da jami'an tsaro suke bakin kokarin su wurin ganin an ceto yaran.

Sannan gwamnan ya bukaci hukumar ilimi ta jihar da ta taimakawa makarantar domin tabbatar da yawan adadin 'yan matan da ba a gansu ba. Sannan kuma su tuntubi iyayen yaran domin samun bayanai da zasu yi amfani dasu a cikin binciken su.

A karshe gwamnan ya jajantawa al'ummar cikin rashin nuna jin dadi akan abinda ya faru, sannan ya tabbatar musu da cewar gwamnatin shi zata yi iya bakin kokarin ta wurin ganin ta samu mafita a al'amarin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng