Wata mata ta haihu a wani gidan rediyon Amurka yayin da take kan aiki
- Wata mata a kasar Amurka ta haihu yayin da take kan aikin watsa labarai
- Ta ce haihuwar ta zo mata mako biyu kafin lokacin haihuwar yayi
- An sanya wa yaron suna Jameson
Wata mata a kasar Amurka, wadda take watsa shirye - shirye a gidan wani rediyo a kasar ta Amurka ta haihu a lokacin da take gabatar da shiri.
Cassiday Proctor, ita ce take gabatar da shirye - shirye na safiya a ranekun mako a wata tashar gidan rediyo da ake kira The Arch a birnin St. Louis na kasar amurka, matar ta bada labarin hanyar da aka bi wajen yi mata tiyata domin cire jaririnta a ranar talatar nan da ta gaba.
DUBA WANNAN: Kasar Saudiyya zata saka kudi $64b, domin samar da wuraren shakatawa
Ta ce nakudar haihuwar ta fara damun ta tun a ranar Litinin. Ta gaya wa manema labarai cewar bata shirya zuwan jaririn ba, saboda ya zo makonni biyu daga lokacin da ake saka ran zuwan sa.
Ms Practor ta ce labarin haihuwar ta ta, shine daya daga cikin labarin da yafi sata farin ciki a dukkanin labaran da take bayarwa a gidan rediyon ga masu sauraron ta. Ta ce labarin haihuwar ya zama tamkar kari ne a kan rayuwar da ta saba gabatarwa yau da kullum, sannan kuma ita ma'abociyar bada labarin rayuwarta ga masu sauraron ta ce.
An sakawa jaririn suna Jameson, bayan da masu sauraron gidan rediyon suka zaba masa sunan a wata gasa da aka gudanar a gidan rediyon a watan Janairun nan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng