Sayayya 2 dana taba yi a rayuwata da ta wuce hankali - Bill Gates
Bill Gates, shahararren hamshakin mai kudin nan da ya kere kowa zurfin aljihu a duniya, ya bayyana wasu sayayya biyu na kyale-kyalen duniya da ya taba a rayuwarsa da suka wuce hankali duk da irin tarin dukiya da yake da ita.
Wannan attajiri shine mai kamfanin nan na Microsoft kuma shine mai gidauniyar nan ta Bill & Melinda Gates Foundation, inda kididdigar bincike ta Bloomberg Index ta bayyana cewa yana da tarin dukiya ta kimanin Dalar Amurka biliyan 91.8.
Bill Gates dai ya bayyana cewa, mallakar wata motar hawa kirar Porsche da kuma jirgin sama domin zirga-zirgar sa sune sayya biyu da ya taba yi a rayuwar sa da suke wuce hankali.

Bincike tare da rahotanni sun bayyana cewa, wannan attajiri ya taka sahun kudi na biliyan tun yana da shekarau 31 a duniya, sai dai wannan zurfi na aljihun sa bai sanya ya shiga wadaka ko almubazzaranci na irin masu hannu da shuni.
KARANTA KUMA: Wata mata ta yashe asusun ta na banki bayan samun labarin mutuwar ta shekaru 5 da suka gabata
A wata ganawa da 'yan jarida, Bill Gates ya bayyana cewa babban burin sa a rayuwa shine biyan ma'aikatan sa albashi domin yiwa iyalan su dawainiya.
Legit.ng ta fahimci cewa, attajiri Bill Gates yana da wani gida alfarma a gundumar Medina ta birnin Washington da kudin sa ya kai kimanin $125m, wanda bai wuci mil daya ba da gidan daya attajirin duniya na biyu wato Jeff Bezos.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng