Aiki dole: Gwamnan Kano ya ki amincewa da murabus din babbar akawuntar jihar
- Babbar Akawun Jihar Kano Hajiya Aisha Bello ta ajiye aikinta
- Tace tana fuskantar shisshigi wurin aiwatar da ayyukanta
- Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya ce ba ta sabuwa
Kamar dai yadda muke samu daga majiyoyin mu, shine cewar gwamnan jihar Kano Alhaji Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ki amincewa da murabus din da babbar akawuntar jihar, Hajiya Aisha Bello ta yi inda ya bukaci ta cigaba da aikin ta.
KU KARANTA: Mafusatan matasa sun jefi ayarin Gwamnan Yobe
Mun samu dai cewa a dazu ne wata takarda ta fita a kafafen yada labarai cewa dauke da cewar babbar akawun ta jiha tana bukatar Gwamnan da ya amince da murabus din na ta.
Legit.ng ta samu dai cewa ta dai mika bukatar ta ta ta ne inda ake tunanin kin bin umurnin ta ne da sauran manyan ma'aikatun jihar ke yi a wajen gudanar da ayyukan ta.
A baya dai mun bayyana maku cewa babbar Akawun Jihar Kano Hajiya Aisha Bello ta ajiye aikinta a yau Alhamis a wata takarda data aikawa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje bisa irin shisshigi da tace tana fuskanta wurin gudanar da ayyukanta daga wasu kusoshin gwamnatin jihar.
Majiyar mu ta rawaito cewa Aisha Bello a shekarar data gabata ta rubutowa gwamnan jihar irin wannan takarda ta ajiye aiki inda ta bayyana dalilin yin haka da cikas da take samu daga gurin wasu manyan gwamnatin jihar da hakan yana hana ta samun ikon gudanar da ayyukan ta bisa yadda ya kamata.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng