Hotunan shugaba Muhammadu Buhari da tsaffin shugabannin kasa bayan ganawarsu a yau
Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar masu a fada a ji na fadin tarayya yau Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, 2017 a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya, Abuja.
Majalisar masu fada a ji wata kwamiti ce da ta kunshi dukkan tsaffin shugabannin kasa, gwamnoni tarayya da yan majalisan zantarwa.
Daga cikin tsaffin shugabannin shugaban kasan da suka hallara sune Janar Yakubu Gowon, Janar Abdussalam Abubakar, da Janar Olusegun Obasanjo.
Rahotanni sun nuna cewa an nemi tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida da Goodluck Jonathan an rasa a taron.
KU KARANTA: Gwamnan jihar Yobe ya ziyarci GSS Dapchi, yace babu ‘yan matan da aka ceto
Har yanzu dai ba'a san abubuwan da wadannan shugabanni suka tattauna ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng