Wata mata ta yashe asusun ta na banki bayan samun labarin mutuwar ta shekaru 5 da suka gabata

Wata mata ta yashe asusun ta na banki bayan samun labarin mutuwar ta shekaru 5 da suka gabata

Wata dattijuwa mai shekaru 62 a duniya, Jackie Dibb, ta yashe gaba daya asusun ajiyar ta na banki, bayan da cikin kuskuren bincike na lafiyar ta.likitoci suka yi mata hasashen mutuwar ta shekaru biyar da suka gabata.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, likitoci sun zartar mata da hukuncin mutuwa tun a watan Nuwamba na shekarar 2016, bayan kuskuren bincike da cewar tana fama da cutar mantuwa a kwakwalwar ta kuma a halin yanzu ba bu magani.

Likitocin dai sun bayyana wa Dibb ta ci karen ta babu babbaka domin kuwa ba za ta wuce shekaru biyar a raye ba, inda ta shiga fagen wadaka da dukiyar da Allah ya bata tare da yin sallama da kuma yin wasiya ga 'yan uwanta musamman jikanyar ta.

Sai dai da yake cuta ba mutuwa ba ce, bayan shekara guda likitoci suka sake nazarin lafiyar ta, inda kuskuren binciken farko ya bayyana da cewar ai babu wata cutar kwakwalwa dake damunta face cutar dimuwa da kuma damuwa irin ta tsaffin mutane.

KARANTA KUMA: Harin Boko Haram ya salwantar da rayuka biyar na farar hula a kasar Kamaru

Legit.ng ta fahimci cewa, a wannan lokaci dattijuwa Dibb ta yashe gaba daya kudaden ta dake asusun ta na banki da su kai Fan 10, 000 wanda a kudin Najeriya sun kai kimanin Naira miliyan biyar da doriya.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, dalibai masu neman shiga jami'o'i a kasar nan sun hurowa hukumar JAMB wuta dangane da rufe rajistar jarrabawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng