Yanzu Yanzu: Yan matan makarantar Dapchi 2 sun mutu a kokarin ceto su da akeyi, sannan kuma har yanzu ba’a ga 13 ba

Yanzu Yanzu: Yan matan makarantar Dapchi 2 sun mutu a kokarin ceto su da akeyi, sannan kuma har yanzu ba’a ga 13 ba

- Rahotanni sun kawo cewa sojoji sun gano gawar yan matan makarantar Dapchi biyu da suka bata

- A ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu ne yan ta’addan Boko Haram suka sace wasu yan mata daga makarantar GGSTC, Dapchi dake jihar Yobe

Rundunar sojin Najeriya sun gano gawawwakin yan matan makarantar Dapchi guda biyu da yan ta’addan Boko Haram suka sace a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, a jihar Yobe, a lokacin da suke kokarin ceto su a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu.

A cewar jaridar Reuters, rahoton ya kuma nuna cewa sojojin Najeriya sun ceto yan matan makarantar guda 76.

Yanzu Yanzu: yan matan makarantar Dapchi 2 sun mutu a kokarin ceto su da akeyi, sannan kuma har yanzu ba’a ga 13 ba
Yanzu Yanzu: yan matan makarantar Dapchi 2 sun mutu a kokarin ceto su da akeyi, sannan kuma har yanzu ba’a ga 13 ba

Legit.ng ta tattaro cewa a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu yan ta’addan Boko Haram sun kai hari makarantar yan mata na Government Girls Science Technical College (GGSTC), Dapchi, jihar Yobe sannan suka sace yan mata da dama.

KU KARANTA KUMA: Barin malamai su rike bindiga zai magance matsalar harbe-harbe - Trump

Tun daga lokacin ana ta samun rahotanni daban-daban wanda ya sha banban da gaskiyar lamarin.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Donald Trump ya bayyana ra’ayinsa akan abun da zai kawo karshen matsalar yawan harbe-harbe da makarantun Amurka ke fuskanta.

Ya ce a ganinsa horar da malamai su iya amfani da bindigogi shine zai kawo maslaha.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng