Hukumar sojin Najeriya ta nada sabon kakaki, ya maye gurbin Kukasheka
Hukumar sojin Najeriya ta canja Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka a matsayin kakakin ta, ta maye gurbin sa da Birgediya Janar Jude Chukwu.
Birgediya Janar Jude Chukwu ne sabon kakakin hukumar sojin Najeriya.
Jude zai maye gurbin Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka, tsohon kakakin hukumar, dake halartar wani kwas a makarantar horon manyan Jami'an gwamnati (NIPSS) dake Kuru, Jos.
Jude na daga cikin kanal din soji 92 da da suka samu karin girma zuwa matsayin Birgediya Janar.
Jude zai kama aiki a lokacin da hukumar soji ke cikin tsaka mai wuya dangane da mabanbantan rahotanni dake zuwa bayan harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai makarantar sakandiren 'yan mata dake Dapchi a jihar Yobe.
KARANTA WANNAN: Ku dawo da kudin gwamnati a yi maku afuwa - Sakon Hukumar JAMB ga macizan da su ka hadiye miliyoyi
Abdullahi Bego, darekta janar na yada labarai a ofishin gwaman jihar, Ibrahim Geidam, ya tabbatar da cewar an ceto 'yan matan makarantar Dapchi kuma suna hannun dakarun sojin Najeriya tare da yin jinjina gare su bisa gaggauta kwato yaran.
Sai dai a wani raddin gaggawa, ma'aikatar tsaro ta kasa ta shaidawa jaridar Premium Times cewar ko kadan bata da masaniyar a kan batun ceto 'yan matan, jawabin da ya saba da wanda Kukasheka ya fitar, inda ya ke nuna cewar an ceto 'yan matan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng