Gwamnan jihar Yobe ya ziyarci GSS Dapchi, yace babu ‘yan matan da aka ceto

Gwamnan jihar Yobe ya ziyarci GSS Dapchi, yace babu ‘yan matan da aka ceto

- Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ya ziyarci GSS Dapchi a ranar Alhamis

- Gaidam ya ce babu 'yan matan da sojoji suka ceto daga hanun Boko Haram

Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, yace babu ‘yan matan makarantar GSS Dapchi da sojoji suka ceto daga hanun Boko Haram

A safiyar ranar Litnini ne ‘yan ta’ada da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai wa GSS Dapchi dake jihar Yobe samame inda suka yi awon gaba da dailbai mata.

Da farko dai gwamnatin jihar Yobe ta ce ba za ta iya tantancewa ba ko akwai daliban da aka sace daga makarantar ba, amma a daren ranar Laraba gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam ya fito ya ce an sace mata a makarantar.

Gwamnan jihar Yobe ya ziyarci GSS Dapchi, yace babu ‘yan matan da aka ceto
Gwamnan jihar Yobe ya ziyarci GSS Dapchi, yace babu ‘yan matan da aka ceto

Ya ce, ya samu labarin cewa sojoji sun samu nasarar ceto ‘yan matan.

KU KARANTA : Rundunar soji ta ba shugaban jam’iyyar APC na jihar Kaduna wa'adin kwanaki uku ya fito ya basu hakuri

A jawabin farko da gwamnan ya fitar ta mai magana da yawun bakin sa, Abdullahi Bego, a ranar Talata, yace rundunar sojoji sun samu nasarar ceto ‘yan matan da ‘yan kungiyar Boko haram suka yi awon gaba da su a makarantar GSS Dapchi a safiyar ranar Talata.

Da gwamnan ya ziyarci makarantar da kan sa a ranar Alhamis, sai ya fadawa mutanen wurin cewa, su cigaba da yin adu’a Allah ya bayyana yan matan da Boko Haram suka sace cikin koshin lafiya.

Yana fadan haka mutanen wurin ya rude mutane suka fara hayaniya da kayar jami'an tsaro suka shawo kan su.

Wani matashi da kanan sa mata guda biyu suna cikin wandanda aka sace yace, gwamann ya yaudare su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng