Harin Boko Haram ya salwantar da rayuka biyar na farar hula a kasar Kamaru
Mayakan Boko Haram sun salwantar da rayuka biyar na fararen hula tare da raunata mutane biyar a wani sabon hari da suka kai Arewacin kasar Kamaru a daren ranar Talatar da ta gaba a yayin ketarewa daga gabar ta Najeriya.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, wannan hari ya afku ne cikin dare a garin Assigashia, inda mayakan suka sheke mutane biyar tare da raunata wasu biyar din kamar yadda ma'aikatan tsaro na kasar suka bayyana.
Legit.ng ta fahimci cewa, Assigashia gari ne dake kan iyaka wajen bayar da dama ta kai tsaye zuwa kasar Najeriya, wanda hare-haren Boko Haram suka afku a lokuta na baya.
Rahotanni sun bayyana cewa, a watan Janairun da ya gabata ne wannan mayaka suka shekar da rayuwar wani farar hula gabar, wanda kawowa sun salwantar da rayuka sama da 2000 na dakarun soji da kuma fararen hula tun daga shekarar 2014 kamar yadda hasashen IGC (International Crisis Group) ya bayyanar.
KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai jagoranci wani muhimmin taro a ranar Alhamis
Wani hasashen ya kuma bayyana cewa, mayakan Boko haram sun salwantar da rayuka sama da 20, 000 tun daga shekarar 2009 da suka dauki makamai da nufin kafa doka ta shari'a.
Najeriya tana iyaka da kasashen Kamaru, Chadi da kuma Nijar, wanda duk yanzu dakarun kasashen sun hada gwiwa domin ganin karshen wannan 'yan ta'adda da tsagerancin su ya kai har ga gabar tafkin Chadi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng