2019: Al’umman Yarbawa sun marama Buhari baya kan ya sake takara karo na biyu

2019: Al’umman Yarbawa sun marama Buhari baya kan ya sake takara karo na biyu

Al’umman Yarbawa mazauna babban birnin tarayya sun kaddamar da goyon bayansu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sake tsayawa takara karo na biyu.

A wata hira da jaridar Leadership a jiya Laraba, 21 ga watan Fabrairu a fadarsa, sarkin Yarbawan Abuja, mai martaba Oba Olusegun Salau ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta yi nasara wajen rage cin hanci da rashawa a kasar.

Salau ya kuma lura cewa gwamnatin ta kuma yi nasara wajen yakar ta’addanci, musamman a yankin arewa maso gabas da sauran yankunan kasar.

2019: Al’umman Yarbawa sun marama Buhari baya kan ya sake takara karo na biyu
2019: Al’umman Yarbawa sun marama Buhari baya kan ya sake takara karo na biyu

Ya jadadda cewa abun da Najeriya ke bukata shine ci gabansa a gwamnati domin gwamnatin ta ci gaba da samun nasarori da kuma kawo ci gaba a kasar, inda kara da cewa gwamnatin zatayi fiye da abun da tayi a karo na biyu.

KU KARANTA KUMA: Ba zamu iya ci gaba da wadannan munanan abubuwa ba – Sultan na Sokoto

Basaraken ya kuma shawarci gwamnatin da ta magance tsadar abubuwa a kasuwa sannan kuma ta cire bara gurbi a gwamnatin, wanda acewarsa suna bata sunan gwamnatin.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen rikicin makiyaya a Najeriya.

Sultan din ya kuma bayyana cewa akwai gagarumin cin hanci da rashawa a Najeriya duk da yaki cin hanci da rashawa da ake yi sannan kuma ya bukaci yan Najeriya da su taimakawa gwamnatin wajen yakar ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng