Ba zamu iya ci gaba da wadannan munanan abubuwa ba – Sultan na Sokoto
- Sultan na Sokoto ya bukaci gwamnatin tarayya da ta magance rickicin makiyaya
- A cewar Sultan, har yanzu Najeriya na gwagwarmaya da gagarumin cin hanci da rashawa
- Ya bukaci yan Najeriya das u daina gauraya laifi da addini ko kabila
Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen rikicin makiyaya a Najeriya.
Sultan din ya kuma bayyana cewa akwai gagarumin cin hanci da rashawa a Najeriya duk da yaki cin hanci da rashawa da ake yi sannan kuma ya bukaci yan Najeriya da su taimakawa gwamnatin wajen yakar ta.
Ya yi wannan jawabi ne a wajen gabatar da wani takarda mai taken Dynamics of Revealed Knowledge and Human Sciences a Abuja, jaridar The Punch ta ruwaito.
Da yake Magana akan rikicin makiyaya a Najeriya, Sultan din yace ba dukkanin Fulani bane makiyaya sannan kuma ba dukka makiyaya bane ke kashe-kashe. Ya bukaci yan Najeriya das u banbance laifi daga addini ko kabila.
KU KARANTA KUMA: Sojoji sunyi ajalin wata daliba bayan sun sa ta tsallen kwado saboda tayi lattin zuwa makaranta
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Babban hafsan sojin tarayya, Laftanan Janar Tukur Y Buratai ya alanta fito-na-fito da makiyaya masu kashe mutane.
Ya ce irin hare-haren da suke kaiwa ya kori manoma 25,000 daga muhallansu a jihar Nasarawa kadai.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng