Babbar kotun tarayya ta sanar da ranar yanke hukunci ga mutumin da ya sanya bama bamai a babban birnin taraya Abuja

Babbar kotun tarayya ta sanar da ranar yanke hukunci ga mutumin da ya sanya bama bamai a babban birnin taraya Abuja

Wata babbar Kotun tarayya dake zamanta a garin Abuja ta sanar da ranar 7 ga watan Maris a matsayin ranar da zata yanke hukunci kan jagoran masu gwagwamarya a Neja Delta, Henry Charles Okah da Obi Nwabueze.

Sahara Reporters ta ruwaito ana tuhumar mutanen biyu ne da laifin sanya bama bamai a babban birnin tarayya Abuja a ranar 1 ga watan Oktobar shekarar 2010, ranar bikin cikar Najeriya shekara 50 da samun yancin kasa, a filin taro na Eagle Square inda mutane 12 suka mutu.

KU KARANTA: Karfin hali: wani mutum ya dambace da wani Maciji sa’annan ya cizge kanta da hakoransa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mai shari’a Gabriel Kolawole ya sanya ranar 7 ga watan Maris ne bayan dukkanin bangarori a shari’ar sun kammala shigar da jawabansu, inda lauyan Okah yace lauyoyi masu kara basu da wata kwakkwarar hujja game da wanda suke karewa.

Babbar kotun tarayya ta sanar da ranar yanke hukunci ga mutumin da ya sanya bama bamai a babban birnin taraya Abuja
Okah a Kotu

Daga nan kuma lauya Emeka Okoroafor ya bukaci kotu ta yi watsi da bukatar lauya mai shigar da kara, kuam ya bukaci kotu ta saki wanda yake karewa, sai dai shi ma lauyan masu shigar da kara, Alex Iziyon SAN ya musanta batun takwarorinsa, inda yace ya san ya gamsar da Kotu fiye da tsammani.

Lauya Alex ya bayyana wanda ake tuhuma, Okah a matsayin dan ta’adda,wanda ya shirya tare da gudanar da hare haren ta’addanci a ranar 1 ga wata Oktoban 2010 a Abuja da yayi sanadin mutuwa mutane da dama, tare da jikkata wasu.

Tun a watan Disambar 2010 ne dai aka gurfanar da Henry Okah, Nwabueze, Edmund Ebiware da Tiemkemfa Francis-Osvwo gaban Kotu kan zarge zargen ta’addanci, inda Francis ya gamu da ajalinsa a daure, yayin da aka yanke ma Ebiware hukuncin daurin rai da rai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng