Gwarzon Dansanda Abba Kyari ya damƙo wuyar shugaban maharan dake kai hare hare a Benuwe da Nassarawa

Gwarzon Dansanda Abba Kyari ya damƙo wuyar shugaban maharan dake kai hare hare a Benuwe da Nassarawa

Allah ya tona asirin shugaban gungun mahara dake kai hare hare a jihohin Benuwe, Nassarawa da Taraba, inda a ranar Laraba, 21 ga watan Feburairu ya shiga hannun jami’an rundunar Yansandan Najeriya.

Gwarzo kuma jarumin dansandan nan, Abba Kyari ne ya jagoranci kama wannan shu’umin mutum, wanda aka bayyana sunansa, Laggi, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

KU KARANTA: Karfin hali: wani mutum ya dambace da wani Maciji sa’annan ya cizge kanta da hakoransa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Laggi ya amsa laifin kai hare hare a garuruwan Tunga, da wasu sassan jihar Benuwe da kuma Nassarawa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutanen da basu ji ba, basu gani ba, tare da janyo asarar dukiyoyi.

Gwarzon Dansanda Abba Kyari ya damƙo wuyar shugaban maharan dake kai hare hare a Benuwe da Nassarawa
Lagge

Idan za’a tuna a baya dai irin wannan hare hare sun yi kamari matuka a yankunan Benuwe, Taraba, Nassarawa da wasu sassan jihar Kaduna, wanda hakan ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari umartar babban sufetan Yansandan na kasa ya tare a jihar Benuwe har sai lamarin ya kwanta.

Hazakali shugaba Buhari ya umarci babban sefatn Yansandan, IG Idris Kpotun da ya tabbata ya kamo masu kai hare hare, a yanzu a iya cewa kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng