Daliban makarantar Firamare 2 sun mutu a Abuja, bayan sun ci biskit a wajen wani taro

Daliban makarantar Firamare 2 sun mutu a Abuja, bayan sun ci biskit a wajen wani taro

Rundunar yan sandan babban birnin tarayya sun tabbatar da mutuwar daliban makarantar firamare na Local Education Authority (LEA), Kubwa II bayan sun ci biskit a wajen wani taro.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa a ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu daliban makarantar biyu, Nehemiah Yahaya da Yahaya Garba masu shekaru 14 daga ajujuwa 5 da 4 na firamare, sun mutu bayan sun ci biskit a wajen wani taro da ba a san wanda ya shirya shi ba.

Kakakin yan sandan hukumar, DSP Anjuguri Manzah, ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa zuwa yanzu ba a kama kowaba yayinda ake ci gaba da gudanar da bincike.

Daliban makarantar Firamare 2 sun mutu a Abuja, bayan sun ci biskit a wajen wani taro
Daliban makarantar Firamare 2 sun mutu a Abuja, bayan sun ci biskit a wajen wani taro

Ya bayyana cewa an tura lamarin zuwa hukumar binciken masu laifi domin bincikar lamarin.

KU KARANTA KUMA: Tattali arziki: Bankuna rututu sun fara ni-‘ya su daga tsarin CBN

Bayan afkuwar lamarin, shugaban yankin Bwari, Mista Musa Dikko ya tsayar da al’amurra a makarantar har zuwa ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu.

Legit.ng ta rahoto a baya cewa dakarun Sojin Najeriya na Briged 13 da ke gudanar da atisayen 'Ayem Akpatuma' wato Tseren Mage da ke yankin Bantaje na karamar hukumar Wukari da ke jihar Taraba sunyi nasarar gano wata bindiga a yayin da suke zagaye a ranar Talata 20 ga watan Fabrairun 2018.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng