Kisan dalibar jami'ar ABU: 'Yan sanda sun cika hannu da mutane biyu
- Jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya a Zaria, jihar Kaduna, sun cafke wasu mutum biyu da ake zargi na da hannu a cikin kisan wani dalibin jami'a
- A ranar juma'ar da ta gabata ne aka kashe wata dalibar ABU, Deborah, bayan an yi mata fashi
- Kakakin rundunar hukumar 'yan sanda a jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu, ya tabbatar da samun daya daga cikin wayoyin dalibar da aka kashe
Hukumar 'yan sandan Najeriya a jihar Kaduna ta tabbatar da damke wasu mutane biyu da take zargi na da hannu a kisan wata dalibar jami'ar ABU Zaria.
An kashe dalibar, Deborah, dake shekarar farko a sashen karatun likitan a dabbobi, a ranar Juma'a a garin Zaria bayan an yi mata fashin wayoyinta na hannu guda biyu.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar an kama daya daga cikin wadanda ake zargin ranar Lahadi yayin da aka kama dayan ranar Litinin, kuma dukkan su na tsare a hannun hukumar 'yan sanda.
Da yake tabbatar da kama wadanda ake zargin, kakakin hukumar 'yan sanda a jihar, Mukhtar Aliyu, ya bayyana cewar sun gano daya daga cikin wayoyin dalibar da aka kashe yayin da suke cigaba da neman daya wayar.
KARANTA WANNAN: Malamin makaranta ya bulale wani dalibi har lahira a Zamfara
"Mun kama daya daga wadanda mu ke zargi a PZ dake garin Zaria, kuma ta dalilin sa ne muka kai ga kama daya mai laifin, sai dai munyi rashin sa'a domin ya riga ya sayar da wayar ga wani barawon zaune," a cewar kakakin na 'yan sanda.
Aliyu ya bayyana cewar tuni suka fara tuhumar masu laifin domin jin dalilin kashe dalibar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng