Har yanzu ba a tantance yawan ‘Daliban da Boko Haram ta sace ba a Yobe - Kwamishinan Ilimi na jihar Yobe

Har yanzu ba a tantance yawan ‘Daliban da Boko Haram ta sace ba a Yobe - Kwamishinan Ilimi na jihar Yobe

- Kwamishinan ilimi na jihar Yobe yace adadin ‘yan matan da ake ce sun bace a kafofin watsa labaru ba gaskiya bane

- Kafofin watsa labaru sun ce dalibai mata 94 sun bace a harin da yan bindiga suka kai wa GSS Yobe

Gwamanatin jihar Yobe ta ce har yanzu bata gama tantance adadin dalibai mata da suka bace ba ta sanadiyar harin da ‘yan bindiga suka kai wa makarantar GSS Yobe a ranar Litinin.

Kwamishinan ilimi na jihar Yobe, Alhaji Mohammed Aminu, yace adadin ‘yan matan da ake ce sun bace a kafofin watsa labaru ba gaskiya bane saboda basu kammala tatanace duka daliban ba.

Har yanzu ba a tantance yawan ‘Daliban da Boko Haram ta sace ba a Yobe
Har yanzu ba a tantance yawan ‘Daliban da Boko Haram ta sace ba a Yobe

A kwai wasu bayanai da ke nuni da cewa ana da ‘dalibai 704 a makarantar, yayin da yanzu haka an samu 610 wanda hakan ke nuni da cewa ba a san inda dalibai 94 suke ba.

KU KARANTA : Jam’iyyar da ba ta fama da rikici matacciya ce - Ado Doguwa

Sai dai Kwamishinan yace wannan kididdiga ba daga hukuma ta fito ba.

A daren ranar Litinin ne wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan ta’adan kungiyar Boko Haram ne suka kai wa makarantar sakandaren mata na GSS Yobe dake garin Dapchi farmaki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng