Wahalar mai: Dalilin da yasa IPMAN suka daina shigo da mai kasar nan
- An dade ana wahalar mai a Najeriya, kuma ana ganin ba zata kare nan kusa ba
- Yan kasuwa sun daina shigo da mai don babu wata riba
- NNPC kadai ke iya samo dalolin shigo da mai
A karshe bara, an sami tsaikon layuka da wahalar mai, wadda ta jefa al'umma cikin tagayyari, da ni-'yasu, inda man kuma yayi tashin gwauron zabi saboda hutu da ake zuwa a wannan lokaci. Ya zuwa yanzu dai, ana ci gaba da samun wahalar man jefi-jefi, sai dai abin yayi rage qamari.
A cewar hukumar NNPC dai a jiya, tana shigo da mai ita kadai, kuma a dan tsakaninnan ta shigo da mai da ya kai na fin Naira tiriliyan daya, kuma tana sanya tallafi wanda baya kasafi kusan N980m a kullum. Batu da ya janyo wa kamfanin fushi da binciken majalisa.
DUBA WANNAN: An haramtawa yara waziffa a tsangayoyi
Majalisar ta binciki kamfanin, inda mai ajiyar kudaden NNPC, Isiaka Razak, yayi kokarin kare kanfanin a jiya, da cewa 'yan kasuwa sun janye hannunsu basu iya shigo da mai kacokan, bisa rashin tabbas na farashin dala, matsalar samun dalar,, da kuma rashin wata riba ta kuzo-ku-gani.
Su dai 'yan kasuwar, sun zargi gwamnati da kin biyansu hakkokinsu, da kuma takure ribarsu bayan wahalarsu ta shigo da man.
A nata bagaren, gwamnati ta ce tana kawo gyara ne bisa yadda ake hada-hadar a da, inda ake tafka sata da cuwa-cuwa da sunan tallaffi koo shigo da mai.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng