Na cika dukkanin muhimman alkawuran da na daukan ma yan Najeriya – Inji shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zuwa yanzu ya cika duk wasu muhimman alkawurran daya daukan ma yan Najeriya a yayin yakin neman zabe a shekarar 2015.
Jaridar The Nation ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne fadar mai martaba Lamidon Adamwa a yayin ziyarar da ya kai jihar Adamawa, inda yace yaki da rashawa da tabbatar da tsaro na daga cikin muhimman alkawurran da ya daukan ma yan Najeriya.
KU KARANTA: An sake kwatawa: Akalla yan mata 94 sun yi ɓatan dabo tun bayan harin da Boko Haram ta kai makarantarsu a jihar Yobe
“Na gamsu da yanayin tsaro a yankin Arewa maso gabas, da ma kasar gaba daya, haka zalika mun ci sa’a manoma mu sun samu albarkar noma sosai da sosai a cikin shekaru biyu da suka gabata. Ina bada tabbacin babban bankin Najeriya za ta cigaba da taimaka manoma.” Inji shi.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Lamidon Adamawa, yace kada shugaban kasa Muhammadu Buhari ya damu da barazanar manyan mutane a Najeriya game da bukatarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a karona biyu.
“Ka jajirce, ka dage, kada ka saurari masu maka barazana game da takararka a 2019, musamman masu kira a gareka kan kada ka sake tsayawa, suna can suna yada karairayi cewa wai Buhari bai tabuka komai ba.” Inji Lamidon
Sa’annan ya zayyano wasu daga cikin nasarorin gwamnatin Buhari da suka hada da tabbatar da zaman lafiya, tsaro, habbaka tattalin arziki da kuma yaki da rashawa, daga karshe kuma yayi kira ga Buhari ya karasa musu aikin kadadar noman shinkafar rani ta Chochi, wanda yace an yi watsi da ita tsawon shekaru 20.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng