Bayan shekaru 5 da haduwa a dandalin sada zumunta, wasu matasa sun shiga daga ciki
A cikin wannan zamani na dandalan sada zumunta, al'amurran rayuwa su kan gudanar, kama daga bayyana ra'ayoyi na siyasa, rikice-rikice, sulhun da kuma kulla alaka ta auratayya tsakanin al'umma.
Da yake hausawa kan ce kaddara ta riga fata, bayan kimanin shekaru biyar da haduwa a dandalin sada zumunta na twitter, wasu matasa sun yi babban rabo da alakar dake tsakanin su ta yi karfin da sakamakon ta ya zamto aure.
Wannan matasa biyu, Fatima da Salim sun kulla abota a yayin da suka hadu da juna a shafukan su na twitter tun a shekarar 2013, wanda daga cikin ikon Mai Duka soyayya ta kama su a sakamakon tarairayar da kuma rainon alakar dake tsakanin su.
Legit.ng ta ruwaito cewa, an daura auren wannan matasa a ranar 16 ga watan Fabrairu a babban birnin kasar nan na garin Abuja.
KARANTA KUMA: An cafke mutane 4 da laifin kisan wani jigo na jam'iyyar PDP a jihar Ribas
Rahotanni sun bayyana cewa, bikin auren wannan matasa ya dauki tsawon lokuta yana gudana a bakunan mutane a sakamakon irin shagulgula na kece raini da kuma bankaye da suka gudanar.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, akwai 'yan majalisar dattawa goma dake neman tayar da zaune tsaye a sakamakon sauya jadawalin zaben shugaban kasa da zai wakana a 2019.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng