YANZU-YANZU: Gamayyar sanatocin Arewa sun cire Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugabansu

YANZU-YANZU: Gamayyar sanatocin Arewa sun cire Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugabansu

Gamayyar sanatocin Arewacin Najeriya sun cire Sanata Abdullahi Adamu mai wakiltar Nasarawa ta yamma. An maye gurbinsa da Sanata Aliyu Wamakko.

Mataimakin shugaban majalisan dattawa, Sanata Ike Ekweremadu ya bayyana wannan ne a yau a filin majalisa.

Zaku tuna cewa a makon da ya gabata, sanata Abdullahi Adamu da wasu sanatoci 9 sun barranta kansu daga sabon dokan canza tsarin zaben da majalisr dattawa tayi.

Kimanin sanatoci 10 a majalisar dattawa ne suka fita daga filin majalisa a fusace bayan an tabbatar da rahoton kwamitin majalisun guda biyu ma gyara dokar zabe a Najeriya.

KU KARANTA: Dalilin da yasa IPMAN suka daina shigo da mai kasar nan

Wadanda suka fusata sunce duk da cewa an tabbatar da wannan doka, sai sunyi iyakan kokarinsu wajen ganin cewa a juyashi.

Sunyi zargin cewa anyi wannan abu ne domin muzgunawa shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban kwamitin majalisan dattawa kan hukumar INEC, Suleiman Nazif, n ya gabatar da wannan rahoto gaban majalisa yau Laraba, 14 ga watan Fabrairu, 2018.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng