Jam’iyyar da ba ta fama da rikici matacciya ce - Ado Doguwa
- Ado Doguwa yayi tsokaci akan rikcin cikin gida da jam'iyyar APC ke fama da shi.
- Doguwa ya ce duk jam'iyyar da bata fama da rikicin cikin gida mataciyya ce
Dan majalissa mai wakiltar mazabar Tudun wada da Doguwa a jihar Kano kuma mai tsawatarwa a majalissar wakillai, Hon.Alhassan Ado Doguwa yace matacciyar jam’iyya ce kadai ba ta fama da rikicin cikin gida a kasashen Afrika.
Hon. Doguwa ya bayyana haka ne a lokacin da yake tofa albarkacin bakin sa akan gidan Sanata Sulaiman Hunkuyi, da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya rusa a ranar Talata.
A loackin da yake zantawa da manema labaru, Hon. Doguwa, ya ce, zai yi wuya a iya kawo karshen rigingimu cikin gida da jam’iyyar ke fusknata a wasu jihohi.
Amma duk da haka Doguwa ya ce, rigimar da ake fama da ita a APC ba za ta hana samun masalaha ba musamman a jihar Kaduna da Sokoto da Kano.
KU KARANTA : Adadin kananan yaran dake fama da yunwa a Najeriya ya Karu
A jiyar ranar Talata gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ba da umurnin rusa gidan Sanata Hunkuyi, wanda ake kallo a matsayin daya daga cikin masu jagorantar sashen jam’iyyar APC na jihar Kaduna dake adawa da gwamnan.
Idan aka tuna baya Legit.ng ta kawo muku labarin aikin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ba, Bola Ahmad Tinubu, na jagorantar kwamitin da zata sasanta barakar dake cikin jam’iyyar APC.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng