Yusuf Buhari na nan da ransa, ku daina yada labaran karya - Onochie
- Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie tace dan shugaban kasa Buhari na nan da ransa cikin koshin lafiya
- Hakan ya biyo bayan jita-jta da ake yadawa na cewa Yusuf ya mutu
Hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta musamman a shafukan zumunta, Lauretta Onochie tayi martini akan rahoton karya dake cewa Yusuf Buhari ya rasu.
Ta bayyana cewa mugun labari dake yawo game da Yusuf Buhari, dan shugaban kasa Buhari da Aisha Buhari karya ne.
Lauretta ta bayyana hakan ne a shafinta na twitter a ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu.
Ga yadda ta rubuta a kasa:
Kamar yadda Legit.ng ta kawo a baya, Yusuf dai yayi hatsari akan babur a babban birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA KUMA: Kada ka saurari manyan kwabo – Lamido ga Buhari
Sannan kuma likitoci dake kula da shi sun tabbatar da cewa yana samun sauki sosai.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng