Sauya fasalin kasa: Jam'iyyar APC tantiran mayaudara ne - Wata Jam'iyyar adawa
Wata jam'iyyar adawa a Najeriya ta Action Democratic Party (ADP) ta yi fatali da rahoton gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya gabatar inda ya bukaci sake fasalin kasa tare da wasu sauye-sauye a makon da ya gabata.
Shugaban na jam'iyyar Action Democratic Party, dai mai suna Mista Yabagi Sani a yayin wata fira da yayi da manema labarai a garin Abuja ya bayyana rahoton a matsayin karin wata yaudara daga cikin kwarewar da jam'iyyar tayi.
KU KARANTA: Sanata Hunkuyi ya baiwa El-Rufa'i martani
Legit.ng ta samu cewa daga nan ne sai ya shawarci 'yan Najeriya da kada su bari jam'iyyar ta rude su da dadin baki irin yadda tayi a shekarar 2015 domin ta samu ta ci zabe.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Benue Mista Samuel Ortom ya bayyana cewa yanzu kam zaman doya da manjan da suke yi da tsohon gwamnan jihar kuma wanda ya gada Mista Gabriel Suswan ya zo karshe bayan samun sulhun da suka yi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a garin Makurdi, babban birnin jihar a jiya Litinin inda ya kuma ayyana tsohon mataimakin shugaban jami'ar tarayya dake Dutsin-ma kuma mai rike da sarautar Tor Tiv mai suna Farfesa James Ayatse a matsayin wanda yayi sanadiyyar sulhun.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng