Mugun shugabanci: Wasu sun fara tattaki daga Legas zuwa Abuja don kyakkyawan shugabanci
- Wasu sun fara tattaki daga Legas zuwa Abuja don kyakkyawan shugabanci
- Kamar yadda muka samu za su yi hakan ne domin nuna adawar su ga salon mulkin shugabannin Najeriya
Wasu 'yan Najeriya da ke a karkashin inuwar wata jam'iyyar siyasa mai suna 'New Nigeria Nationalists NNN' a turance sun dunguma tare da fara tattaki a kasa daga jihar Legas dake yankin kud maso yammacin kasar nan inda suka kuma nufi garin Abuja domin nuna adawar su ga salon mulkin shugabannin Najeriya.
KU KARANTA: Jirgin saman Dana ya shiga daji da fasinjoji
Su dai wadannan mutanen sun bayyana cewa sun cika jikkunan su da guzuri sun kuma sha alwashin zuwa garin na Abuja a kasa domin nuna rashin jin dadin su game da yadda 'yan Najeriya ke shan bakar azaba kullu yaumin saboda rashin kyakkyawan shugabanci.
Legit.ng ta samu dai cewa shugaban ayarin, Mista Yinka Quadri ya kuma bayyana cewa sun kuduri niyyar cimma burin nan nasu ne a cikin kwanaki 45.
A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a ta hannun kamfanin dake kula da albarkatun man fetur na Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) a takaice ya bayyana cewa kawo yanzu ya shigo da fetur da ya kai na $5.8 biliyan.
Hukumar ta Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban ta Dakta Mai Kanti Baru yayin da yake ansa tambayoyi a gaban kwamitin majalisar dattijai dake sa ido game da harkokin hukumar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng