Gwamnatin tarayya ba zata sayar da matatun man fetur ba - Kachikwu

Gwamnatin tarayya ba zata sayar da matatun man fetur ba - Kachikwu

- Ibe Kachikwu, karamin ministan man fetur na kasa, ya ce gwamnatin tarayya ba zata sayar da matatun man fetur ba

- Ya ce burin gwamnatin tarayya shine Najeriya ta zama cibiyar tace man fetur ta nahiyar Afrika

- Ministan na wadannan kalamai ne a yau, Talata, yayin wani taro a kan hanyoyin bunkasa harkar man fetur da sinadarin iskar gas

Ibe Kachikwu, karamin ministan man fetur na kasa, ya ce gwamnatin tarayya ba zata sayar da matatun man fetur dinta ba.

Kachikwu ya bayyana cewar burin gwamnatin tarayya shine Najeriyata ta zama cibiyar tace man fetur ta nahiyar Afrika.

Karamin ministan na man fetur na wadannan kalamai ne a yau, Talata, yayin wani taro domin bunkasa masana'antar man fetur da sinadarin iskar gas, a Abuja.

Gwamnatin tarayya ba zata sayar da matatun man fetur ba - Kachikwu
Karamin Ministan Man fetur, Dakta Ibe Kachikwu

Ya kara da cewar gwamnatin tarayya zata gyara lalacewar da hanyoyin gudanawar danyen man fetur ta yi domin ganin matatun man fetur da ma'adanan sa dake fadin kasar nan sun dawo aiki yadda ya kamata.

Maimakon sayar da matatun man fetur din, gwamnatin tarayya zata gyara tare da inganta su domin jawo hankalin masu saka jari a bangaren.

DUBA WANNAN: Masana tarihi a Amurka sun fitar da jerin shugabannin kasar 10 da suka fi kwazo a mulki

"Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya riga ya fadi cewar ba zai sayar da matatun man fetur ba, saboda idan zamu sayar da su a halin da suke ba zamu samu riba ba," inji Kachikwu.

Kachikwu ya cigaba da cewa "tsarin da muka bullo da shi shine na kiran 'yan kasuwa da zasu gyara matatun da kudinsu. Mun kusan kammala wannan shirin domin kwanan nan zamu sanar da wadanda suka yi nasarar samun wannan kwangilar."

A ranar Litinin, Kachikwu, ya ce burin gwamnatin tarayya shine Najeriya take samar da kaso 14% zuwa 90 na man fetur da ake amfani da shi a Najeriya cikin watanni 18 zuwa 20 masu zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng