Fusatattun matasa sun sauke fushinsu akan wani Coci inda aka ɗaura ma wani Saurayi aure da ƙanwarsa

Fusatattun matasa sun sauke fushinsu akan wani Coci inda aka ɗaura ma wani Saurayi aure da ƙanwarsa

Wani abin kazanta ya faru a kauyen Agba na jihar Anambra, inda aka daura auren wani matashi mai suna Chiadi Ezeibekwe tare da kanwarsa ta jinni mai shekaru 17 bayan ya dirka mata ciki.

Sai dai wannan lamari bai yi ma matasan kauyen dadi ba, inda suka far ma Cocin da aka daura auren cikin fushi, mallakin yayan Angon da Amaryar, Fasto Chijike, suka banka masa wuta, ya babbake kurmus.

KU KARANTA:

Legit.ng ta ruwaito matasan sun dauki wannan mataki ne saboda a cewarsu wannan abin kunya ne, musamman ma yadda aka daura auren a coci, mai suna ‘Shepard of Dwelling Fullness of God Church’, inda Faston ya yi nuni ga Aya na 6 cikin sura ta 36 na littafin Baibul, wanya yace ya bada damar aure tsakanin yan gida daya.

Sai dai masana sun ce babu wannan ayar a Baibul. Hakazalika mabiyan Faston sun yi masa nuni ga aya ta 9 cikin sura ta 18 na cikin Baibul dake hani da aure tsakanin yan gida daya. Sai dai ko da wani dan uwansu ya kira taron gaggawa, sai mahaifin ma’auratan yace ‘Abin gama y agama.”

Bugu da kari mahaifiyarsu ma ta yaba da auren, tare da jinjina ma yayan nata, inda tace addininsu ya halasta, sai dai da kakarsu ta samu wannan labara, sai ta gayyaci dukkanin yayan nata da jikokin nata don jin yadda aka haihu a ragaya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng