Yan sanda sun kama mutane 2 da ake zargi da kisan dalibin ABU
Rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna tace ta kama wadansu mutane biyu dake da hannu a kisan wani dalibi a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.
“Mun kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan dalibin ABU; an kama daya a ranar Lahadi yayinda aka kama dayan a ranar Litinin,” kakakin rundunar, Muktar Aliyu ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Talata, 20 ga watan Fabarairu a Kaduna.
Yace masu laifin na amsa tambayoyi sannan za a mikasu zuwa kotu bayan an kammala bincike.
KU KARANTA KUMA: Hukumar SUBEB ta hana wazifa a makarantun Tsangayar
NAN ta ruwaito cewa an kashe marigayin wanda ya kasance dalibin karatun likitan dabbobi a ranar Juma’a.
A wani lamari na daban Legit.ng ta samu labari cewa a halin yanzu Jam’iyyar APC ta shiga halin ba-kan-ta a Jihar Kogi inda har ta kai Gwamnan Jihar ya nada wasu sababbin Shugabannin Jam’iyyar a Jihar a makon da ya wuce.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng