Najeriya ta kaddamar da yada kalaman batanci a matsayin ta’adanci
- Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da yada kalaman batanci a matsayin ta’adanci
- Lai Mohammed ya ce duk wanda aka kama da laifin yada kalaman batanci za a mishi hukunci irin na 'yan ta'adda
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da yada kalaman batacin a matsayin ta’adanci, ta ce zata gurfanar da duk wanda aka kama yana yada kalaman batanci.
Ministan Labaru da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana haka a ranar Litinin, inda ya ce hukuma zata hukunta duk wanda aka kama da laifin yada kalam batanci kamar dan ta’ada.
Ministan ya bayyana haka ne a taron da kungiyar kafofin watsa labaru NUJ suka gayyaci shi a jihar Kano.
Mohammed ya tunatar da su cewa dokar gurfanar da kafofin watsa labaru da suka dauki nauyin yada kalaman batanci yana nan.
KU KARANTA : Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta kashe naira miliyan N65 akan shafin yanan gizo
Bayan haka dan majalissa wakilai dake wakiltar mazabar, Gumel, Gagarawa da Megatiri, Mohammad Sani Soro, yayi kira da majalissar dattawa ta sanya dokar hana yada kalaman batanci a kafofin sada zumunta na zamani.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng