Yaduwar Musulunci a Turai babbar barazana ce ga Kiristanci - Viktor Orban
Firaministan kasar Hungary,Viktor Orban ya bayyana cewa idan har Turawa basu farka daga mafarkin da suke yi da wuri ba, to watan rana za a wayi gari Musulunci ya mamaye yammacin duniya.
A cewar Viktor: "Sanin kowa ne, al'adun Turawa na canzawa, al'umar Kirista na kara raguwa a kullun, manyan biranen Turai kuma na ci gaba da Musulunta.
“Idan har muka zuba ido muna kallo ba tare daukar kwakwaran matakai ba, wata rana za'a wayi gari addininmu, al'adunmu, kai hatta da wayewarmu zasu gushe daga duniya kamar basu taba kasancewa ba.
“Domin a kullun,musuluntar da yammcin duniya, shi ne babban burin da Musulmai suka sa gaba.
“Idan muka yi sake, sai munanan mafarkanmu sun tabbata gaskiya.Yankinmu na ci gaba faduwa, amma yammacin duniya bata ankara da wannan kawo yanzu.
“A nan gaba, ba wai a kudu kawai ba, Musulunci zai samun gindin zama a yamma da kuma tsakiyar Turai.
“Yaduwar Musulunci a Turai da kumma yammacin duniya, babbar annoba ce ga Kiristanci.Dole ne mu daura damarar hana yaduwar ta a yankunanmu ta hanyar kin bai wa duk wani mai neman mafaka ya tsalake iyakokin kasashenmu."
KU KARANTA KUMA: Abubakar Tureta ya kasance mutun mai nagarta – Shugaba Buhari
Orban ya furta wadannan kalaman a yayin babban taron da ake shiryawa a Budapest babban birnin kasar Hungary domin tattauna batun masu neman mafaka.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta’aziyya akan marigayi malamin musulunci, Abubakar Tureta, inda yabayyana shi a matsayin mutun mai tarin sani da kyawawan hallaya wanda yayi rayuwarsa wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin mutane mabiya addini daban-daban.
A wata sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin malamin, shugaban kasa Buhari yace marigayin yayi rayuwa mai cike da gaskiya, za a kuma dunga tunawa da gudunmawar da ya bayar a rayuwarsa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng