Cin hancin N1m na biya ma'aikata na shigo da bindigogi 661

Cin hancin N1m na biya ma'aikata na shigo da bindigogi 661

- Ya bada cin hanci an bashi damar shigo da bindigogi Najeriya

- An kama shi da laifin shigo da bindigogi 661 a shekarar data gabata

- An gurfanar dasu a gaban kotu dashi da abokan shi da ake tuhuma da laifin shigo da makaman

Ya bawa hukumomin tsaro cin hancin N1m sun bashi damar shigo da bindigogi 661
Ya bawa hukumomin tsaro cin hancin N1m sun bashi damar shigo da bindigogi 661

Mahmud Hassan, daya daga cikin wadanda ake tuhuma da laifin shigo da bindigogi 661 cikin kasar nan ta haramtacciyar hanya, watan Disambar bara, ya shaidawa kotun tarayya cewar ya bawa jami'an hukumar 'yan sandan farin kaya, da sauran hukumomin tsaro cin hanci na naira miliyan daya, inda ya samu damar shigowa da bindigogin.

DUBA WANNAN: Zamu sayar da kadarorin da muka kwato a hannun barayin gwamnati - Buhari

Hassan, tsohon ma'aikacin kwastan, wanda yayi ritaya, ya bayyana hakan a cikin wani bidiyo da aka yi a lokacin da hukumar DSS su ke yi masa tambayoyi. Bidiyon da aka fitar ranar 27 ga watan Maris, shekarar 2017, daga karfe 2 na rana zuwa karfe 2 da minti 45 na rana, wanda wani jami'in DSS, Jaiye Emmanuel, ya bayar dashi , a lokacin da ake yin shari'ar shi a kotu jiya.

"Na bada N1m domin a fito mini da kwantainar daga cikin tashar," inji shi a bidiyon.

Da aka tambaye shi yadda aka raba N1m din, yace: "An bawa masu bincike wato (Examiners) N200,000, C.I.O. N100,000, Enforcement N200,000, 'Yan sanda da SSS an bawa wasu N20,000, N25,000 wasu kuma N30,000, sannan masu gadin kofa kuma N200,000, kofar fita, N20,000, sai kuma kofar karshe N50,000."

Haka kuma Hassan ya shaidawa masu binciken a bidiyon cewa ya amince da shi da mai shigo da bindigogin akan zai bashi N3.8 miliyan, inda shi kuma ya bukaci N4 miliyan da ya ji cewar bindigogi ne a cikin kwantainar.

Idan ba a manta ba a ranar 14 ga watan Yuni, shekarar 2017 majiyar mu Legit.ng ta taba kawo muku rahoto cewar, hukumar kwastan ta gurfanar da Mahmud Hassan da Salisu Danjuma, tare da Oscar Orkafor, Donatus Ezebunwa Achinulo da kuma Matthew Okoye, a gaban kotun alkali Ayotunde Faji's, da laifin shigo da makamai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng