Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta kashe naira miliyan N65 akan shafin yanan gizo
- Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta yi ikrarin kashe naira miliyan N65m akan shafin yanan gizo
- Boss Gida Mustapha shine sabon sakataren gwamnatin tarayya da shugaba Buhari ya nada a watan Oktoba na shekara 2017
Ofishin sakataren gwamnatin tarayya, SGF, ta yi ikrarin kashe naira miliyan N65m akan shafin yanan gizo a shekara 2017.
Legit.ng ta samu rahoton cewa an ware wa ofishin sakataren gwamnatin tarayya naira miliyan N65m daga kasafin kudi akan aikin shafin yanan gizo, kuma ofishin tayi ikrarin kashe naira N64m daga cikin kudin.
Ofishin ta ce har yanzu tana kan sayo kayan aikin kafa yanan gizo.
Boss Gida Mustapha, shine sakataren gwamnatin tarayya na yanzu da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nada shi a watan Oktoba na shekara 2017 bayan ya sauke tsohon sakataren gwamnatin tarayya,Babachir David Lawal, bisa zargin cin hanci da rashawa.
KU KARANTA : Wasu mambobin jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zanga a ofishin jam’iyyar dake Abuja dan nuna rashin goyon bayan Oyegun
Har yanzu Legit.ng ta kasa gano wanda ya kaddamar da kwangilar a tsakanin tsohon SGF, Babachir David Lawal, da SGF na yanzu, Boss Gida Mustapha.
Masana kimiyya sun ce, ba zai taba yiwuwa a kashe makudan kudade irin wannan wajen gina shafin yanan gizo ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng