Zamu sayar da kadarorin da muka kwato a hannun barayin gwamnati - Shugaba Buhari
- Shugaba Buhari ya bayyana cewar gwamnatin tarayya zata sayar da kadarorin da ta kwace a hannun barayin gwamnati
- Ya bayyana hakan ne a jiya a gidan sa dake garin Daura jihar Katsina
- Ya yi alkawarin bunkasa harkar noma da samar da wutar lantarki ga al'umma
A jiya litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin tarayya za ta sayar da kadarorin da ta kwace a hannun barayin gwamnati, sannan za ta saka kudin a cikin bitalamalin gwamnati. Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ga 'yan majalisar masarautar Daura, lokacin da suka kai mashi ziyara a gidan sa dake Daura cikin jihar Katsina.
DUBA WANNAN: Gwamnatin Tarayya zata bayyana wadanda zasu saka hannun jari a sabbin matatun man fetur da ake ginawa - Kachikwu
Shugaba Buhari ya bayyana cewar, mutane da dama da ake zargin su da satar dukiyoyin gwamnati suna nuna cewar ba dukiyoyin su bane. Ya bayyana cewar bai yi mamaki ba da yawan da suke karawa ba, na nuna cewar ba dukiyoyin su bane, saboda matakan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa take dauka ga duk wanda ta kama da irin wannan laifin.
"Shekarun baya da suka wuce, akwai abokina wanda muka yi firamare tare, kafin ya rasu ya taba fada mini cewa akwai lokacin da zai zo wanda barayin gwamnati zasu dinga guduwa suna barin dukiyoyin su, to ga lokacin yazo yanzu, inda zaka ga ma'aikacin gwamnati da gidaje 10 a Abuja, Kaduna, wasu ma har da kasashen ketare." Saboda haka babu gudu babu ja da baya, za muyi ta bin duk wata hanya domin ganin mun kwato dukiyoyin gwamnati.
Idan har kuna biye damu zaku ga cewar an kama wasu daga cikin wadannan barayin gwamnatin, sannan kuma ga wadanda suka musanta cewar ba kayan su bane, zamu sayar da kayan mu saka kudin a cikin bitalamalin gwamnati.
Shugaban kasar ya yi alkawarin cewar, gwamnati zata yi kokari wurin ganin takin noma ya samu ga manoma, domin samun cigaba ta bangaren noma a kasar nan.
Ya ce, "yana cigaba da bawa 'yan Najeriya hakuri, saboda muna iya bakin kokarin mu, kuma muna fatan daminar wannan shekarar ta zo da albarka, za mu yi kokarin kara kudi akan harkar noma domin ganin mun samar da taki ga manoma. Har ila yau, za mu cigaba da gina hanyoyi, zamu samar da wutar lantarki, hanyoyin jirgin kasa, da sauran su."
Shugaban kungiyar da suka kawo mashi ziyarar, Muhammad Sale, ya bayyana wa shugaban kasar cewar, sun zo su yi mishi ta'aziyya ne bisa rashin da yayi na 'yan uwa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng