Ya kamata a ce kawo yanzu Obasanjo yana kurkuku - Sanata Abdullahi Adamu

Ya kamata a ce kawo yanzu Obasanjo yana kurkuku - Sanata Abdullahi Adamu

- Ya kamata a ce kawo yanzu Obasanjo yana kurkuku - Sanata Abdullahi Adamu

- Ya ce bai da bakin magana da har zai bude yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Ya ce kamata yayi a ce Cif Obasanjo yana gidan wakafi domin irin ta'asar da ya tafka

Shugaban gamayyar yan majalisar dattijan kasar nan da suka fito daga arewacin Najeriya da kuma ke wakiltar mazabar jihar Nasarawa ta yamma mai suna Sanata Abdullahi Adamu a jiya yayi wa tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar, Cif Obasanjo wankin babban bargo.

Ya kamata a ce kawo yanzu Obasanjo yana kurkuku - Sanata Abdullahi Adamu
Ya kamata a ce kawo yanzu Obasanjo yana kurkuku - Sanata Abdullahi Adamu

KU KARANTA: Shin ko akwai yan Boko Haram a cikin gwamnatin Buhari?

Sanatan wanda kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa ne ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ko kusa bai da bakin magana da har zai bude yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika yana sukar salon mulkin sa.

Sanata Abdullahi Adamu, da har ila yau jigo ne a jam'iyyar APC mai mulki ya bayyana cewa yanzu ma kamata yayi a ce Cif Obasanjo yana gidan wakafi domin irin ta'asar da ya tafka lokacin yana shugaban kasa ba ta misaltuwa.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yana da yakinin cewa kasar Najeriya zata cigaba sosai shi yasa ma yake a raye da tuni ya bi ta wata hanyar ya kashe kan sa.

Haka zalika tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa babu wani mahalukin da ya isa ya hana shi fadar albarkacin bakin sa game da yadda lamurran kasar ke tafiya a ko yaushe indai har yana numfashi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng