Dandalin Kannywood: Ko na yi aure zan cigaba da harkar fim - Hannatu Bashir
- Ko na yi aure zan cigaba da harkar fim - Hannatu Bashir
- Jarumar dai ta kuma ayyana cewa kawo yanzu ita ba ta da wata sana'ar da take yi wadda ta wuce harkar fim
- Jarumar ta bayyana cewa kawo yanzu ta fito a cikin fina-finai akalla 50 a tsawon shekaru 7
Daga daga cikin fitattun fuskoki a fafajiyar masana'antar shirya-fina-finan Hausa ta Kannywood mai suna Hannatu Bashir ta fito ta bayyana cewa ita fa ko da ta yi aure to tabbas zata cigaba da harkokin ta na fim musamman ma bangaren shiryawa da sauran ayyukan bayan fage.
KU KARANTA: Saura kiris sojoji su kama Shekau aka umurce su su janye
Fitacciyar jarumar dai ta kuma ayyana cewa kawo yanzu ita ba ta da wata sana'ar da take yi wadda ta wuce harkar fim din sannan kuma a shirye take ta bar fitowa a cikin fina-finai watau 'aktin' za zarar ta samu miji ta kuma yi aure.
Legit.ng ta samu haka zalika cewa jarumar ta yi karin haske game da batun da ake na cewa mafi yawancin 'yan matan da ke yi harkar fim 'yan iska ne inda ta bayyana cewa sam ba haka bane domin kuwa da yawa daga cikin wadanda ake kamawar ba 'yan fim din ne ba.
Da karshe ne kuma sai jarumar ta bayyana cewa kawo yanzu ta fito a cikin fina-finai akalla 50 a tsawon shekaru 7 da ta shafe tana harkar kuma fim fin 'Kotun Ibro' shine fim din ta na farko.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng