Dandalin Kannywood: Shugaba Buhari ya gaza ta kowane fanni na shugabanci - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Shugaba Buhari ya gaza ta kowane fanni na shugabanci - Fati Muhammad

- Shugaba Buhari ya gaza ta kowane fanni na shugabanci - Fati Muhammad

- Ta nuna rashin jin dadin ta game da yadda ta ce wasu na zagin su kawai domin sun fadi ra'ayin su

- Jama'a da dama sun yi ta mayar wa da tsohuwar jarumar martani inda suka yi kaca-kaca

Daya daga cikin tsofaffin fuskoki kuma fitattun jarumai a masana'antar shirin fim din Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood watau Fati Muhammad ta fito a wani salo irin na siyasa ta zazzage dukkan abun da ke ran ta game da shugaba Muhammadu Buhari.

Dandalin Kannywood: Shugaba Buhari ya gaza ta kowane fanni na shugabanci - Fati Muhammad
Dandalin Kannywood: Shugaba Buhari ya gaza ta kowane fanni na shugabanci - Fati Muhammad

KU KARANTA: Daliban makarantar kwana sun tserewa harin Boko Haram

Kamar dai yadda muka samu daga wasu kafafen sadarwar zamani, tsohuwar jarumar ta bayyana cewa shugaban kasar ya gaza a dukkan fannonin shugabanci inda kuma ta kara da cewa ba za su ja bakin su suyi shiru ba.

Legit.ng ta samu cewa jarumar haka zalika ta nuna rashin jin dadin ta game da yadda ta ce wasu na zagin su kawai domin sun fadi ra'ayin su inda ta cigaba da cewa ba za ta yi kasa a gwuiwa ba ko ta dena.

Haka nan ma kuma ta bayyana takaicin ta game da yadda ta ce a shekarar 2015 da suka fito suka nunu kauna ga shugaban ba bu wanda ya nuna masu yatsa amma sai yanzu da suke ganin ya gaza.

Sai dai tuni wasu jama'a da dama sun yi ta mayar wa da tsohuwar jarumar martani inda suka yi kaca-kaca da ita asoshiya midiya din.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng