Zagon kasa: Saura kiris sojojin Nigeria su cafke Shekau aka umurce su suka janye
- Saura kiris sojojin Nigeria su cafke Shekau aka umurce su suka janye
- An dai samu tabbacin hakan ne a wani faifen bidiyon da wakilan ta suka samu
Kamar dai yadda majiyar mu ta tabbatar, kafar yada labaran nan ta kasar Ingila watau BBC ta samu cewa saura kiris dakarun sojin Nigeria su kusa su samu nasarar cafke jagoran kungiyar nan ta 'yan Boko Haram, Abubakar Shekau a wani samamen ba zata da suka kai amma sai shugabannin sojojin suka dakatar da su.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari makarantar mata a Yobe
Kafar labaran ta BBC dai ta bayyana cewa ta samu tabbacin hakan ne a wani faifen bidiyon da wakilan ta suka samu daga hannun wasu dake fafutika tare da sojojin Najeriyar.
Legit.ng dai ta samu cewa a cikin faifan bidiyon, an nuna yadda dakarun sojin na Najeriya ke ta safa-da-marwa a wasu sansanonin wucin gadi a dajin Sambisa da ake kyautata zaton shugaban 'yan ta'addan na a boye.
Sai dai kamar yadda muka samu, sojojin ba su dade ba suna wannan sintirin sai aka dakatar da su inda kuma bayan kwanaki kamar hudu da dakatarwar sai mayakan Boko Haram cikin motoci dauke da abubuwa masu fashewa sun kai wa sojojin hari.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng