2019: Rashin lafiya ce kaɗai za ta hana Buhari tsayawa takara - Kalu

2019: Rashin lafiya ce kaɗai za ta hana Buhari tsayawa takara - Kalu

Tsohon gwamnan jihar Abia, Dakta Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa, rashin lafiya kadai ce za ta hana shugaban kasa Muhammadu Buhari sake neman takara a zaben 2019 mai gabatowa.

A daren ranar Lahadin da ta gabata ne Kalu ya bayyana hakan a yayin ganawa da 'yan jarida a farfajiya ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake garin Legas, inda ya ce a halin yanzu dai babu wata tantama shugaba Buhari a shirye yake.

Yake cewa, "shugaba Buhari amintaccen mutum ne mai gaskiya da rikon amana, kuma zai zayyanawa 'yan Najeriya kudirin sa na sake tsayawa takara ko kuma kishiyar hakan. Muna dai yi masa fatan samu koshin lafiya da zai sauke nauyin da rataya a wuyan sa."

Orji Uzor Kalu

Orji Uzor Kalu

"Kun san cewa Buhari mai sanin ya kamata ne, idan har ya tabbatar lafiyarsa ba za ta ba shi dama na sake neman takara to kuwa ba zai ko fara ba."

Tsohon gwamnan ya ci gaba da cewa, "Buhari yana matukar kwazo, misali daya kuwa shine babbar gadar Neja da ake ginawa a halin yanzu."

KARANTA KUMA: 'Yan majalisar Buhari dake hanƙoron kujerar gwamna a jihohin su

Kalu ya kuma kirayi shugaba a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, akan ya kara kaimi wajen sulhuntanta rikita-rikitar dake jam'iyyar.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, akwai jerin kasashe goma mafi arhar rayuwa a nahiyyar Afirka, wanda Najeriya ba ta sahun su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel