Karambani: Wani Dan kasuwa ya caccaka ma Maigidansa kwalba

Karambani: Wani Dan kasuwa ya caccaka ma Maigidansa kwalba

Wani matashi dan kasuwa Chinedu Akajiofor mai shekaru 39 ya fasa kwalbar giya sa’annan ya caccaka ma Maigidansa Gdfrey Nhayiba, wanda hakan yayi sanadiyyar kanwatar da Maigidan a Asibiti.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito an gurfanar da Akajiofor a gaban wata kotun Majistri dake Ikeja a jihar Legas a ranar Litinin, 19 ga watan Feburairu, sai dai ya musanta aikata laifin.

KU KARANTA: Kaico! Yadda wata Uwa da ɗanta suka kashe wani ƙaramin Yaro mai shekaru 5 a Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dansadan mai kara, Inspekta Victir Eruadaa ya shaida ma Kotu cewa wand aake tuhumar ya aikata wannan aika aika ne a ranar 6 ga watan Nuwamba a gidansu mai lamba 94 titin AIT, Ungywar Alagbado.

Dansanda yace Akajiorfor ya caccaka ma Maigidan nasa kwalbar ne a kirjinsa tare da lakada masa dan banza duka biyo bayan wata cacar baki da ta kaure tsakaninsu. Sai dansanda yace wanda ake tuhuma ya tabbatar masa da cewa ya dauki wannan mataki ne saboda Maigidan nasa ya ce masa ‘Dan kungiyar asiri’

Wannan laifi ya ci karo da sashi na 172 da 166 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Legas, wanda ya tanadar da hukuncin daurin shekaru 3 a gidan Yari ga duk wanda ya aikata laifin, kamar yadda Dansanda ya fadi.

Daga karshe Alkali G.O Anifowoshe ta bada belin wanda ake tuhuma akan kudi N50,000 tare da wani jigo da zai tsaya masa, shi ma akan N50,000, sa’annan ta dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Maris.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng