Kaico! Yadda wata Uwa da ɗanta suka kashe wani ƙaramin Yaro mai shekaru 5 a Kaduna

Kaico! Yadda wata Uwa da ɗanta suka kashe wani ƙaramin Yaro mai shekaru 5 a Kaduna

Wani lamari mai muni ya faru a jihar Kaduna, inda aka samu wata muguwar mata tare da danta suka saci wani kamaranin yaro, jikarta, suka kashe shi, sa’nnan suka binne shi a dakinsu, inji rahoton Aminiya.

Wannan lamari ya faru ne a unguwar Hayin Danmani cikin karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna, inda matar mai suna Lalai da danta Bala suka shiga hannun jami’an Yansanda bayan asirinsu ya tonu.

KU KARANTA: Babban lauyan gwamnati ya shawarci Buhari ya dakatar da EFCC daga binciken tsohuwar minista Diezani Allison da Bello Adoke

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Lalai da Bala sun saci yaron ne mai suna Walid Adamu yayin dayake kan hanayarsa ta zuwa Islamiyya da nufin karbar fansa daga hannun iyayensa, amma daga bisani suka halaka shi, tare da binne gawar a dakin Bala.

Kaico! Yadda wata Uwa da ɗanta suka kashe wani ƙaramin Yaro mai shekaru 5 a Kaduna

Lalai da Bala

Mahaifin Walid ya bayyana ma majiyarmu cewa: “Walid ne da nan a uku cikin yayana guda hudu, yana kan hanyarsa ta zuwa Islamiyya ne suka dauke shi, da yan uwansa suka koma gida, sai suka ce basu ga Walid ba, aka yi ta nema babu labara, har sai karfe uku ne matar ta kira wayar Yayana tana bukatar N300,000 kudin fansae Walid, idan bah aka ba zasu kashe shi.”

Sai dai a lokacin, Malam Adamu mai sana’ar tuka motar siyar da ruwa bashi da N300,000, bayan wani lokacin suka sake kira wai sun rage kudin zuwa N150,000 daga nan kuma suka kuma ragewa N20,000.

Malam Adamu ya bayyana cewa bayan an aika musu da kudin a asusun banki da suka turo, sai Bala ya aika wani yaro da zai siya wayar hannu a wajen ya tafi ya ciro N15,000, da zuwansa banki sai Yansanda suka kamashi, inda shi kuma ya nuna iyayen Bala, har ma da Balan duk aka kama su.

Majiyar ta ruwaito Lalai ce ta umarci Bala ya yanka Walid saboda ya gane su, shi kuma yace ba zai yiya ba, sai Lalai ta sanya guba a abinci ya ci ya mutu, bayan nan suka binne shi a dakin Bala.

Sai dai Yansanda sun sako yaron mai siyar da wayar, da kuma mahaifin Bala bayan sun tabbatar basu da hannu cikin lamarin, sa’annan sun ce da zarar sun kammala bincikezasu gurfanar da su gaban Kotu, kamar yadda Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Aliyu Muktar ya tabbatar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel