Labarin yadda ta kwashe a gaban Kotu tsakanin wata Uwa da mutumin da ya hallaka mata yaro

Labarin yadda ta kwashe a gaban Kotu tsakanin wata Uwa da mutumin da ya hallaka mata yaro

Wata mata mai suna Rukiye Abdul-Mutakallam ta baiwa kowa mamaki a yayin zaman wata kotu dake kasar Amurka, inda aka ake sauraron karar wasu matasa da suka bindige mata danta har lahira.

Wannan lamari ya faru ne a ranar 28 ga watan Yunin shekarar 2015 a garin South Cumminsville na kasar Amurka, yayin da Suliman, tsohon Soja a rundunar Sojan ruwa ta kasar Amurka ke kan hanyarsa ta zuwa gida.

KU KARANTA: Babban lauyan gwamnati ya shawarci Buhari ya dakatar da EFCC daga binciken tsohuwar minista Diezani Allison da Bello Adoke

Yana cikin tafiya ne sai Javon, Valentino da wani abokinsu suka harbe shi, sa’annan suka kwashe kudaden dake aljihunsa, tare da dauke ledar abincin da ya siyo zai kai ma matarsa dake jiransa a gida, duk abinnan kudin dake aljihunsa basu wuce dala 60 ba.

Labarin yadda ta kwashe a gaban Kotu tsakanin wata Uwa da mutumin da ya hallaka mata yaro
Rukiye da hoton Suliman

A yanzu haka Kotu ta yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru da dama, sai dai wani abin ban mamaki shi ne yadda uwar mamacin, Rukiye ta fashe da kuka tana tausayin matasan, inda ta rungume su tare da daukan alkawarin kai musu ziyara a kai a kai, saboda yara ne, kuma tana fatan za ta canza musu hali.

Rukiye tace ramuwar gayya game da yaran ba zau dawo mata da danta Suliman ba, “Allah ya riya ya kaddara mutuwarsa, watakila wannan ce hanyar shiryuwarsu.” Kamar yadda majiyar Legit.ng ta jiyo.

Labarin yadda ta kwashe a gaban Kotu tsakanin wata Uwa da mutumin da ya hallaka mata yaro
Daya daga cikin masu laifin

Rikiye mai shekaru 66 ta cigaba da cewa “Duk da cewa sun kashe min da na, ya dace mu dage akansu don kawar musu da wannan mummunan hali idan sun fito daga gidan Yari, idan ba haka ba wata rana zasu kashe kansu ma gaba daya.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng