Badakalar $11.489m: Babu wani sulhun boyen da zamuyi da ke - EFCC ta bayyanawa Patience Jonathan
Hukumar hana almundanan da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, ta yi watsi da bukatan Uwargidan tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan, na sulhu kan kudi $11,489,069.03 da aka samu a asusun bankin ta.
Hukumar EFCC ta bukaci tsohuwar uwargidan shugaban kasa ta gabatar da kanta gaban kotu kafin sulhu bisa ga dokan kasa.
Hukumar ta bayyana cewa ba zata yi musharaka a wani sulhun da kotu ba ta da ilimi a kanta ba.
Kana, hukumar EFCC har yanzu ta gaza bibiyan mutane 29 cikin 31 na kamfanonin da suka turawa Patience Jonathan kudi.
Wata majiyar EFCC ta bayyana cewa: “Mun duna wasikar Patience Jonathan na ranan 30 ga watan Junairu, muna ganin cewa bukatanta na sulhun boye sabon abu ne kuma abin zargi.
KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta saukaka mana hanyoyin cin zaben 2019 – Makarfi
Muna masu watsi da bukatarta saboda hukumar EFCC bata musharaka cikin irin wannan sulhu. Da zai fi mata ta gabata a gaban kotu bisa ga doka idan tana son sulhu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng