Zaben 2019: Sarakunan gargajiya sun yanke shawarar goyon bayan Buhari

Zaben 2019: Sarakunan gargajiya sun yanke shawarar goyon bayan Buhari

Sarkin Maradun na jihar Zamfara mai suna Alhaji Garba Tambari ya kwarmatawa 'yan jarida cewar tuni shi da wasu sauran sarakunan gargajiya a dukkan fadin kasar nan sun yanke shawarar goyawa shugaba Muhammadu Buhari baya a zaben shekarar 2019.

Sarkin na Maradun yayi wannan ikirari ne a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan da gama ganawa da shugaban da a halin yanzu yake wata ziyara a garin sa na Daura dake a jihar Katasin.

Zaben 2019: Sarakunan gargajiya sun yanke shawarar goyon bayan Buhari

Zaben 2019: Sarakunan gargajiya sun yanke shawarar goyon bayan Buhari

KU KARANTA: Tsohon minista ya koma APC daga PDP

Legit.ng ta samu cewa Alhaji Garba haka zalika ya bayyana cewa dukkan mai son cigaban kasar nan to a halin yanzu dole ne fa ya goyi bayan shugaba Buhari din don ya zarce.

A wani labarin kuma, Kamar dai yadda muke samu daga majiyoyin mu, tsohon ministan wasanni a zamanin mulkin jam'iyyar adawa ta yanzu ta People Democratic Party (PDP) a jihar Kebbi mai suna Alhaji Sama'ila Sambawa ya jagoranci dumbin magoya bayan sa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Alhaji Sambawa wanda a baya ya rike matsayin minista a lokutta da dama a karkashin mulkin PDP ya bayyana sauya shekar ta sa ne a ranar Lahadi a babban filin wasa na Halidu dake a cikin Birnin Kebbi, babban birnin jihar ta Kebbi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel