Rikita-Rikita: Majalisar tarayya ta bukaci Ministan Buhari ya ajiye mukamin sa

Rikita-Rikita: Majalisar tarayya ta bukaci Ministan Buhari ya ajiye mukamin sa

Wani dan majalisar tarayya a majalisar wakillai mai wakiltar mazabar Ijebu-North/Ijebu-East/Ogun na jihar Ogun mai suna Honarable Adesegun Adekoya ya yi kira ga ministan sufurin kasar nan Mista Rotimi Amaechi da yi murabus daga mukamin sa.

Honarable Adesegun Adekoya ya yi wannan kiran ne a zauren majalisar ranar Alhamis din da ta gabata inda ya bayyana cewa matsayin da yake rike da shi na jagorancin kamfe din shugaba Muhammadu Buhari na zaben 2019 ya dauke masa hankali.

Rikita-Rikita: Majalisar tarayya ta bukaci Ministan Buhari ya ajiye mukamin sa

Rikita-Rikita: Majalisar tarayya ta bukaci Ministan Buhari ya ajiye mukamin sa

KU KARANTA: An kama barawa dumu-dumu cikin jirgi

Legit.ng ta samu cewa Honarable Adesegun Adekoya wanda kuma dan jam'iyyar adawa ta PDP ne yayi wannan kiran ne ga ministan yayin da ya ke ansa tambayoyi lokacin da halarci zaman kwamitin sufuri na majalisar.

A wani labarin kuma, Sarkin Maradun na jihar Zamfara mai suna Alhaji Garba Tambari ya kwarmatawa 'yan jarida cewar tuni shi da wasu sauran sarakunan gargajiya a dukkan fadin kasar nan sun yanke shawarar goyawa shugaba Muhammadu Buhari baya a zaben shekarar 2019.

Sarkin na Maradun yayi wannan ikirari ne a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan da gama ganawa da shugaban da a halin yanzu yake wata ziyara a garin sa na Daura dake a jihar Katasina.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel