Halin bera: An kama kasurgumin barawo dumu-dumu yana sata cikin jirgi a Najeriya
Jami'an hukumar tsaron kasar nan ta 'yan sanda dake a filin sauka da tashin jirage na kasa-da-kasa dake a jihar Legas na tunawa da Murtala Muhammad sun tabbatar da kama wani kasurgumin barawo dumu-dumu da laifin sata a cikin jirgi a ranar asabar din da ta gabata.
Haka nan kuma mun samu cewa jirgin da aka kama barawon a cikin sa dai na kamfanin Air Peace ne mai lamba P47139 kuma yana kan hanyar sa ne ta zuwa Abuja daga Legas din.
KU KARANTA: Sule Lamido ya bude ofishin yakin neman zabe
Legit.ng dai ta samu cewa an kama barawon ne yayin da aka samu wasu bandiran kudi 'yan dubu-dubu makare a cikin jakar sa wanda da kuma aka tambaye shi yaushe ya fara satar a cikin jirgi sai ya ce a wannan shekarar.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Ekiti Mista Ayo Fayose ya bayyana takaicin sa game da yadda yace wasu shanu na makiyaya sun ne mi su kawo wa jirgin sa a jihar Ondo cikas yayin da yake so ya sauka a filin sauka da tashi na jirage a garin Akure.
Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a shafin sa na dandalin sada zumunta na Tuwita inda ya bayyana cewa shanun sai da suka hana jirgin sauka na tsawon mintuna 15 kafin daga baya ya samu ya sauka a ranar Lahadin da ta gabata.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng