Kisa a jihar Zamfara: 'Yan sandan Najeriya sun kama mutane 3
Jami'an tsaro na hukumar 'yan sandan Nijeria ta bayyana cewa ta samu nasarar kama akalla wasu mutane uku da take zargin su da hannu dumu-dumu a kashe-kashen da suka auku a baya-baya nan da aka yi a jihar Zamfara dake a arewa maso yammacin kasar nan.
Yan sandan dai a cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun kakakin hukumar, CSP Jimoh Moshood ya bayyana cewa mutanen da suka cafke haka zalika suna bada hadin kai a bincike da 'yan sanda suke yi.
KU KARANTA: Makiyaya sun kashe zakuna 3
Legit.ng ta samu haka zalika cewa sanarwar ta cigaba da bayyana cewa da zarar hukumar ta 'yan sandan sun kamala binciken da su ke yi , za a gurfanar da mutanen a gaban kotu.
Wadanda ake zargin dai sun hada Halilu Garba mai shekara 45 da Zubairu Marafa mai shekara 45 da kuma Nafi'u Badamasi mai shekara 40.
A wani labarin kuma, Sarkin Maradun na jihar Zamfara mai suna Alhaji Garba Tambari ya kwarmatawa 'yan jarida cewar tuni shi da wasu sauran sarakunan gargajiya a dukkan fadin kasar nan sun yanke shawarar goyawa shugaba Muhammadu Buhari baya a zaben shekarar 2019.
Sarkin na Maradun yayi wannan ikirari ne a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan da gama ganawa da shugaban da a halin yanzu yake wata ziyara a garin sa na Daura dake a jihar Katasin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng