An hallaka wata shu’umar dabba dake cin mutane da dabbobi a jihar Kano
An yi nasarar kasha wata shu’umar dabba mai kama da kerkeci da ta bulla a garin Beli dake karamar hukumar Rogo.
Jaridar rariya ta rawaito cewar dabbar na cin naman dabbobi, karnuka, hard a ma mutane.
Bayan cin dabbobi da mutane, rariya t ace dabbar na bacewa a neme ta a rasa bayan ta kama mutum ko dabba.
Dabbar na da matukar zafin nama wajen kama mutum ko dabba kuma muddin ta kama mutum ko dabba to sai dan buzun sa domin kuwa ba mai iya kubutar da su.
DUBA WANNAN: 2019: Hotunan taron bude ofishin takarar Sule Lamido a mahaifar sa
Jaridar Rariya bata ambaci ko dabbar ta hallaka wani mutum ba ko kuma tun yaushe dabbar ta bulla a garin ba. Kazalika basu ambaci yadda aka kai ga kasha dabbar ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng